download: Pdficon.png
Odticon.png
Version: 2.1

Baptisma

Labarin

(Matiyu 3:11; 13-17; 18-20)

Kafin Yesu ya fara koyaswa da warkaswa, ya je kogin Urdun domin a yi masa Baptisma. Akwai wani Anabi mai suna Yahaya shine mai kiran mutane su juyo daga zunubansu domin mai Ceto ya kusato. Yesu shine mai ceton da suke jira.

Yesu bai taba yin zunubin da zai tuba ba. amma ya so Yahaya ya yi masa Baptisma, Yesu ya bamu tabbaci cewa ya yarda da koyaswa Anabi Yahaya. daga farko Yahaya bai so yayi wa Yesu Baptisma ba, shi ya sa ya ce wa Yesu “Kai nake so ka yi mini baptisma” Yahaya ya sani cewa, Yesu ya fi shi girma shi yasa ya karba umurni daga wurin Yesu kafin ya yi masa baptisma.

Yohaya ya yi wa Yesu Baptisma. Yesu ya nutse cikin rowan, a lokacin da Yesu yake fitowa daga cikin rowan sai muryar Ubangiji daga sama ta ce “Wannan shine Dana wanda nake kauna: Da shi nake farin ciki”.

Yesu ya umurce almajiransa su je su almajirantad da dukan al’umai sunayi masu Baptisma a cikin sunan Allah Uba da Da da Ruhu Mai Tsarki. Su kuma koya wa mutane yin biyaya da duk abubuwanda ya koya masu. Almajiran sun yi duk kamar yadda Yesu ya umurce su, duk inda sun tafi, suna yin baptisma ma wadanda sun karbi Yesu.

Kwaikwayo: Sake bada labarin!

Tambayoyi

  1. Menene ka koyi daga wannan labarin Baptisma?
  2. Me ya kamata kayi biyaya ga?

Ma’anar Baptisma

Kalmar “Baptisma” tana nufi “A nusar, ko biso” wankewa, ko tsarkakewa. Kamar yadda aka yi wa Yesu Baptisma, haka nan kuwa duk wadanda suka gaskanta dashi ya kamata suyi Baptisma. Yesu ya umurce almajirensa suyi wa masu gaskantawa dashi Baptisma a cikin sunan Allah Uba da na Da, dana Ruhu Mai Tsarki” (Matiyu 28:19). Karin haske a cikin Ayuka Manzani 2:28:

Bitrus yace, kowanenku ya tuba daga zunubarsa, ya juyo wurin Allah, domin ayi masa Baptisma a cikin sunan Yesu, domin gafaran zunubi, da kuma samun ikon Ruhu Mai Tsarki.

Tsarkakewa cikin sunan Allah uba...

Furcin zunubai da tuba

Mu furta zunubanmu mu kuma juyo daga garesu. Kadda mu boye zunubanmu mu palashe su (1Yahaya 1:9). Mu yi furci a inda mun sani ba mu yi daidai da nufin Allah ba. Mu roke Allah ya gafarta mana, mu kuma dakatar da kanmu daga yin zunubi. Da taimakon Allah zamu chanza halayenmu mu kuma bi Nufin Allah.

Tsarkakewa cikin sunan dan...

Baptisma ta ruwa a cikin sunan Yesu Kristi

Ana kiran Baptisma ta ruwa “haihuwa ta biyu” (Titus 3:5). Romawa 6:1-11 an kwatantashi kuma da biso, kamar yadda aka bisine Yesu ya kuma tashi zuwa rai, haka muke shiga cikin ruwan Baptisma abinne mu, mu tashi zuwa tsabon rayuwa tare da yesu. Mun bisine tsohon halitarmu ta zunubi, an yantas damu daga zunubi. Manufar shine babu zunubi a cikin mu. Yanzu, mun zama “Sabon halita ” (2Korontiyawa 5:17).

Tsarkakewa cikin Ruhu Mai Tsarki...

Karba Ruhun Allah

Allah yana so ya bamu Ruhu Mai Tsarki. Ruhu Mai Tsarki shine “karfin Allah” zuwa gare mu: Yana taimakonmu cikin bin Allah, da kuma yin nasara kan shaidan. Shi yake sa yayan ruhaniya kamar kauna, murna, salama da hakuri. (Galantiyawa 5:22).
Idan mun karba Ruhu Mai Tsarki, wani sabon hali zai shiga rayuwanmu. Misali: Ayukan Manzani 19:6 (zamu same baye baye na ruhaniya) (1Korintiyawa 12:1-11 da 14:1-25). Baye bayen Ruhu Mai Tsarki domin goyon bayan masubi, a cikin aikin bishara da suke yi. Saboda mutane suga ikon Allah a cikinsu.

Ka shirya domin ayi Baptisma?

Zaka iya yi wa bangaskiyarka biki a lokacin baptisma.

  • Yaushene za ka yiaptisma?
  • Wa da wa zaka gayata?
  • A ranar da za’a yi maka Baptisma, za ka iya shirya wata labari game da rayuwarka. yadda Yesu ya cece ka daga zunubi, ya baka rai na har abada.

Kowa ya shirya lokacin da za’a yi masa Baptisma tun da lokaci. Ka karanta tambayoyin Baptisma ka shirya kowane tambaya.

Tambayoyin Baptisma

  1. Ka hurta zunubanka wa Allah?
  2. Ka sani da kuma bangaskiya cewa an gafarta maka dukan zunubanka ta wurin mutuwar Yesu?
  3. Ka shirya domin ka binne tsohowar rayuwarka, ka kuma karba tsabuwar rayuwa agun yesu?
  4. Ka kudurta zaka yi tafiya tare da Yesu babu fasawa ko juya da baya?
  5. Zaka ci gaba da bin Yesu ko da aka yi maka ba’a duka, iyayenka sun koreka daga gida, da kuma fuscantar kalubale?
  6. Kana so ka karbi Ruhu Mai Tsarki?